NIS ta samar da fasfo 204,332 cikin makonni 3.

Hukumar shige da fice ta Nijeriya (NIS) tace ta samar da fasfo 204,332 cikin makonni uku.

Da ta ke yiwa manema labarai jawabi a Abuja, Mukaddashiyar Kwanturola Janar ta NIS, Mrs Caroline Wuraola-Adepoju ta ce, kalubalen da hukumar ke fuskanta a yanzu shi ne, mutane 91,981 ne kacal cikin adadin suka karbi fasfo din su.

Ta bayyana cewa, an samu wannan nasarar ne sakamakon kafa dokar ta-baci kan samar da fasfo akan lokaci yayin da ta amshi ragamar shugabancin hukumar a watannin da suka gabata.

A cewarta, zuwan sabon ministan harkokin cikin gida, wani kwarin guiwa ne hukumar ta samu wurin zage damtse domin ganin an shawo kan kalubalen samar da fasfo akan lokaci.

Don haka, shugabar ta yi kira ga ’yan Nijeriya da suka bukaci fasfo din da su zo su amshi abinsu ba tare da sake biyan ko taro ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *