Yan Sanda Sun kama mawaki Naira Marley kan mutuwar Mohbad

An cafke Azeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley, domin yi masa tambayoyi da sauran bincike dangane da mutuwar Mohbad.

Hakan ya fito ne daga bakin Benjamin Hundeyin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Legas.

Hundeyin ya tabbatar da hakan ne cikin wata sanarwa a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Talata, 3 ga watan Octoban 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *