“Mun kashe ƴan-awaren Biafra guda 2 da tarwasa sansanoninsu a jihar Imo” Sojojin Najeriya

Sojojin Kasarnan sunce sun kashe ƴan-awaren Biafra guda biyu da tarwasa sansanoninsu a jihar Imo.

A ata sanarwa da rundunar sojin Najeriyar ta wallafa a shafinta na Twitter, tace yayin samamen da dakarunta suka kai, sun kuma gano abubuwan fashewa da ƴan awaren Biafran ke amfani da shi.

Sunce sun ɗauki tsawon lokaci ana artabu tsakaninsu da ƴan ƙungiyar ta IPOB, kafin daga bisani suci karfinsu tare da raunata da dama.

Sojojin sun gano cewar ƴan IPOB  na amfani da sansanonin wajen cin naman mutane da yin tsafi da kuma sanya tsoro a zukatan mutane.

Har ila yau, sanarwar tace an lalata gidajen wasu bokaye guda biyu tare da kama huɗu daga cikinsu.

Sojojin sun kara da cewar sun ƙwato wata tankar mai da babura huɗu da faifen zuko hasken lantarki da kuma kuɗaɗe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *