Wata kungiyar matasa a garin Potiskum na jihar Yobe ta gudanar da zanga-zangar lumana da tattaki kan yawaitar matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.
Kungiyar ta ce ta dauki matakin ne don nuna fushinta da yadda ake yi wa yara mata fyade, garkuwa da mutane da kuma tabarbarewar ilimi a Arewa, a ranar Talata.
Da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar Karamar Hukumar Potiskum, shugaban kungiyar, Kwamared Aliyu Haruna ya ce “Mun fara wannan zanga-zangar lumana ne duba da yadda ilimi ya tabarbare a Arewa da kuma matsalar tsaro da ke addabar al’umma da yadda ake yi wa kananan yara da ’yan mata ’ya’yan talakawa marasa galibu fyade ana barin su ba su da wata madafa.”
Ya kara da cewa, “A matsayinmu na matasa, mun damu da halin da suke ciki don sanar da jama’a hakan ta hanyar zanga-zangar lumana don kyautata rayuwar ’yan uwanmu masu zuwa.