Kotu ta yi fatali da korafin PDP kan zaben gwamnan sakkwato

Kotun sauraron korafe-korafen zabe ta yi fatali da karar da jam’iyyar PDP ta shigar tana kalubalantar nasarar zaben Gwamna Aliyu Ahmed na Jihar Sakkwato.

Kotun ta ce korafin da dan takara na jam’iyyar PDP, Sa’idu Umar ya shigar yana kalubalantar sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris ba shi da tushe ballantana makama.

Ana iya tuna cewa, Hukumar Zabe ta Kasa INEC ce ta ayyana Aliyu Ahmed na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara.

Sai dai dan takarar na jam’iyyar PDP ya shigar da korafin cewa an saba wa Dokar Zabe sannan kuma abokin takarar wanda INEC din ta bai wa nasara bai cika sharudan tsayawa takara ba.

Sai dai dan takarar na jam’iyyar PDP ya shigar da korafin cewa an saba wa Dokar Zabe sannan kuma abokin takarar wanda INEC din ta bai wa nasara bai cika sharudan tsayawa takara ba.

A cikin hukuncin da kotun mai alkalai uku ta yanke a wannan Asabar karkashin jagorancin Mai Shari’a Haruna Mshelia, ta ce korafin da dan takarar na PDP ya shigar bai karbu saboda ya gaza gabatar da gamsassun hujjoji.

Gabanin soma zaman yanke hukuncin, jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), sun iyakance wakilan gidajen jaridun da za a bai wa damar halarta a harabar Babban Kotun da ke Sakkwato.

Jami’an wadanda suka ce umarni aka ba su daga sama, sun ba da dama ce kadai ga Gidan Talabijin na Kasa (NTA), Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) sai kuma wakilan gidajen jaridu mallakin Gwamnatin Sakkwato.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *