Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya jaddada aniyar rundunar sojin Najeriya na kawo karshen kalubalen tsaro a kasarnan.
Musa ya bayyana haka ne a wata ziyarar bangirma da ya kai wa Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli a yammacin ranar Juma’a a garin Zariya na jihar Kaduna.
Ya kuma ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba kalubalen tsaro da kasarnan ke fuskanta zai zama tarihi, kuma ya nemi a yi wa sojoji addu’ar samun nasara.
Musa tare da wasu manyan hafsoshin soji sun yi ta’aziyyar rasuwar wasu masallata takwas, wadanda suka mutu a wani masallaci.