Hukumar kwastam ta yi nasarar kame tsuntsayen aku 105 da kudinsu ya kai naira miliyan 24.9

Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) reshen Seme a yammacin ranar Juma’a ta bayyana cewa jami’anta sun kama aku guda 105 da wasu tsuntsaye da suka fito daga Togo da Jihar Katsina wadanda kudinsu ya kai Naira miliyan N24,912,928.00.

A cikin wata sanarwa da ta fito daga babban kwamandan hukumar ta Kwastam, Kwanturola Timi Bomodi, rundunar ta ce tuni aka tsinci gawarwakin tsuntsaye 10 daga cikin 105 da aka kama a lokacin da jami’an hukumar ta Kwastam suka tare motocin da ke dauke da su ta hanyar Seme-Badagry.

A cewar shugaban Kwastam na yankin Seme, “Na yi farin cikin maraba da ku baki daya zuwa hukumar kwastam ta Najeriya, da ke yankin Seme, da wurin zama na Seme-Krake Joint Border Post, wanda ke kan gaba wajen kasuwanci a yammaci da tsakiyar Afrika, kuma daya daga cikin mafi yawan layin iyaka a Afirka.

“A ranakun 27 da 28 ga watan Satumba da misalin karfe 21:00 da 12:00 ne jami’an hukumar kwastam ta Najeriya reshen Seme da ke sintiri a kan hanyar Seme zuwa Badagry, suka tare wata motar bas da ta taso daga Togo zuwa Najeriya,da kuma wata daga Katsina zuwa Jamhuriyar Benin.

“Binciken da aka yi wa wadannan motocin bas din ya nuna cewa an gano Korayen aku guda 60, Akun Budgerigar guda 14, Akun Rosella na Gabas guda 6, Akun Macaw Biyu, Farin Akun Cockatoo guda daya, Akun Rose Ringed Parakeets, sai kuma Tsuntsun Maidain Dock, Tsuntsayen Soyayya Uku da wasu tsuntsaye hudu.

Sannan “kimanin 10 daga cikin wadannan tsuntsayen sun mutu sakamakon raunin da suka yi na safarar su a cikin wannan hali.

Tribune Online ta rawaito cewa tuni hukumar ta kame wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen safarar tsuntsayen.

“Akun da sauran Tsuntsaye an biya musu kudin haraji (DPV) na Naira miliyan N24,912,928 kawai.”

Shugaban Hukumar Kwastam, Compt. Bomodi ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika da wasu daga cikin al’umma suka yi, ya kuma nanata cewa cinikayyar namun daji ya saba wa yarjejeniyar ciniki ta kasa da kasa kan namun daji da na flora (CITES) wadda yarjejeniya ce ta duniya tsakanin gwamnatocin da Najeriya ta rattaba hannu a kai.

Kwanturolan ya ci gaba da cewa wadanda suka aikata wannan haramtaccen fatauci za su ci gaba da haduwa da fushin hukumar muddin suka ki tsayawa daga hanyar Legas zuwa Abidjan.

Kamar yadda hukumar kwastam ta Najeriya ta umarci hukumar kwastam na inganta hadin gwiwa tsakanin hukumomin, an mika Akun da sauran tsuntsayen da aka kama ga jami’an hukumar kula da gandun daji ta kasa domin aikinsu ne na gyarawa da kare su daga cutar da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *