Gwamnatin Najeriya ta amince da sayo jiragen yaki masu saukar unguku har guda 12 domin tunkarar matsalar tsaro

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da sayo jiragen yaki masu saukar unguku har guda 12, domin tunkarar matsalar tsaro da ta dade tana addabar kasar nan.

Babban hafsan sojin Nijeriya, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, shi ya bayyana haka a wajen bude taron kara wa juna sani na harkokin jiragen sama na sojojin Nijeriya da ya gudana a Abuja inda ya ce Rundunar za ta yi amfani da jiragen yakin masu saukar ungulu  wajen yin shawagi a sararin samaniya domin magance kalubalen tsaro da ke addabar kasar nan.

Ya ce, jirage masu saukar ungulu guda 12 za su fara aiki da sashin kula da zirga-zirgar jiragen sama na sojojin Nijeriya, wanda aka kafa domin inganta karfin sojojin kasa da daukar dawainiyar aiki da kuma inganci yayin gudanar da ayyuka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *