Yau Laraba ne Al’ummar Musulmin duniya ke gudanar da bukukuwan ranar Maulidin Nabiyy

Yau Laraba ne Al’ummar Musulmin duniya ke gudanar da bukukuwan ranar Maulidin Nabiyy, ko kuma tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW) kamar yadda aka saba yi kowacce ranar 12 ga watan Rabiu Awwal shekarar hijriyya.

Bisa yadda aka saba, akan shirya tarurruka inda malaman addinin Islama ke gabatar da kasidu akan tarihin Manzon Allah (SAW) domin fadakar da jama’a irin kyawawan halayen fiyayyen halitta da kuma irin gwagwarmayar da ya yi wajen gabatar da sakon manzancin da Allah subhanahu wata’ala ya aiko shi ga al’ummar duniya baki daya.

Yayin gudanar da irin wadannan tarurruka, daliban makarantu kan rera baitukan yabo ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) domin karramawa da kuma fadakar da matasa akan irin gudunmawar da ya bayar wajen isar da sakon annabta da kuma muhimmancin karrama shi tare da nuna kauna ga iyalan gidansa.

A kowacce shekara kasashen Musulmi da dama kan bada hutu a irin wannan rana domin gudanar da irin wadannan bukukuwan Mauludi a birane da ƙauyuka.

Tuni dai gwamnatin tarayya ta ware wannan rana ta Laraba a matsayin ranar hutu domin bada damar gudanar da bukukuwan Maulidin a hukumance, yayin da yanzu haka aka fara gudanar da bukukuwan a garuruwa da dama.

Wasu jama’a kan yi amfani da watan na  Rabiu Awwal baki dayansa wajen gudanar da bikin Maulidin a garuruwa daban daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *