Wike, ya taya daukacin mazauna babban birnin tarayya murnar bikin Mauludi,

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Barista Nyesome Wike, ya taya daukacin mazauna babban birnin tarayya murnar bikin Mauludi, inda ya bukace su da su bi tsarin zaman lafiya, tausayi da hadin kai a tsakaninsu.

A sakonsa na bikin Mauludi ga mazauna garin, Ministan ya bukaci al’ummar Musulmi da sauran mazauna babban birnin tarayya Abuja da su hada kai, su yi amfani da bikin a matsayin wata dama da za su sake jaddada aniyarsu ta juriya, soyayya da kyautatawa kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya koyar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ministan ya sanya wa hannu da kansa, wadda aka raba wa manema labarai a Abuja ya bukaci mazauna babban birnin dasu taimakawa yunkurinsa na dawo da martaba da birninke dashi a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *