“Tsarin samar da kudade ne ke haddasa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya”. – Sabon gwamnan CBN

Sabon gwamnan babban bankin kasa CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa tsarin samar da kudade ne ke haddasa hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya.

Sabon gwamnan ya kuma bayyana cewa, zai yi fatali da wasu tsare-tsaren magabacinsa, Godwin Emefiele, sannan zai mayar da hankali kan tsare-tsaren samar da kudade don karfafa darajar Naira.

Cardoso wanda ya bayyana haka ne a yayin tantance shi tare da tabbatar da shi a matsayin gwamnan CBN a ranar Talata, ya kuma amince cewar babban bankin na fuskantar kalubale da dama, amma sai daiya sha alwashin cewar da shi da mataimakansa zasu mai da hankali wajen gano matsalolin tare kuma da daukar matakan warware su.

Mataimakan gwamnan da aka tantance kuma aka tabbatar da su, sun hada da: Emem Usoro, Abdullahi Dattijo, Bala Bello da Philip Ikeazor.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *