Tinubu ya bukaci al’umma da su yi wa kasar addu’o’i

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci al’umma da su yi wa kasar addu’o’i yayin da musulman duniya ke murnar zagayowar ranar haihuwar annabi Muhammad (SAW).

A cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan yada labaru, Ajuri Ngelale, Tinubu ya ce “Najeriya tana a wani lokaci mai muhimmanci na wanzuwarta, yayin da gwamnati ke daukan duk wasu matakai na ciyar da kasar gaba, ana bukatar tallafi daga al’umma ta hanyar nuna kishin kasa, da juriya da kuma addu’o’i.”

Haka nan shugaban ya kuma bukaci al’ummar musulmi da su yi koyi da halayen fiyayyen halittun ba a lokacin murnar maulidin ba kawai, har ma da sauran lokuta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *