Wani sashe na ginin kotun kolin kasar nan ya kama da wuta a safiyar yau Litinin

Wani sashe na ginin kotun kolin kasar nan ya kama da wuta a safiyar yau Litinin, duk da cewa ba a sami asarar rai ba.

Jami’in hulda da jama’a na kotun, Mista Festus Akande, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce musabbabin gobarar wutar lantarki ce daga daya daga cikin ofisoshin alkalai kuma an kashe ta ne ta amfani da na’urorin kashe gobara da ke ginin.

Akande ya kara da cewa labaran da ake yadawa a shafukan sada zumunta na cewa an samu asarar rayuka “labari ne na karya”.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 6 na safiya.

Rahotanni sun bayyana cewa masu aikin share share ne da ke bakin aiki da wasu ma’aikatan da suka koma bakin aiki da wuri suka gano gobarar tare da sanar da hukumomi.

An ce ma’aikatan sun yi amfani da na’urorin kashe gobarar da ke ginin wajen kashe gobarar.

Gobarar dai ta kama ofisoshi uku ciki har da na Mai shari’a Mohammed Saulawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *