Majalisar dattawa ta yi kira da a gaggauta ceto daliban Gusau da wasu ‘yan bindiga suka sace.

Majalisar dattawa ta yi kira da a gaggauta ceto daliban jami’ar tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara da wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a san ko su wanene ba suka sace.

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojoji, Sanata Abdulaziz Yar’Adua ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa a Abuja.

Ya ce ceto daliban mata da ba su ji ba ba su gani ba daga hannun ‘yan bindigar, dole ne ya zama babban fifikon kasar nan a yanzu.

‘Yar’Adua ya koka da cewa matsalar ‘yan fashi da tayar da kayar baya da masu aikata laifuka a kasar nan ke yi tare da sace ‘yan kasa da ke bin doka da oda wata babbar barna ce ga martabar kasar nan da kuma tunanin hadin kan ‘yan Najeriya.

Ya ce dole ne sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro su kasance da isassun kayan aiki cikin gaggawa, domin dakile matsalar  da tuni ke barazana ga hadin kan kasa, da zaman lafiya da kuma ci gaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *