Hukumar NYSC: “Muna kan kokarin dawo da sauran masu bautar kasa dake hannun barayi”

Darakta-Janar na hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC), Brig-Gen. Yush’au Ahmed ya bayar da tabbacin cewa, ana ci gaba da kokarin ganin an sako wasu ‘yan bautar biyar da aka sace a Zamfara.

Ahmed ya bayyana hakan ne a wani zama na tattaunawa da kwamitin majalisar wakilai kan ci gaban matasa a ranar Alhamis a Abuja

Ya bayyana cewa daga cikin mutane takwas da aka yi garkuwa da su a watan Agustan 2023 a kan hanyarsu ta zuwa sansanin wayar da kan jama’a a jihar Sokoto, an sako uku.

Shugaban ya ce, dukkanin hukumomin tsaro da abin ya shafa suna aiki tare da shugabannin gargajiya da na addini don ganin an sako mutanen biyar.

Muna yin kokari don ganin mun fitar da yaran daga garkuwa. Daga dukkan alamu da muke samu, muna fatan za mu same su da wuri,” inji shi.

Ahmed ya ce an mayar da masu bautar kasar zuwa babban birnin tarayya Abuja kuma an ba su kulawar da ta dace.

Shugaban hukumar ya ba da shawarar a guji yin tafiye-tafiye da daddare yana mai cewa hakan ya saba wa ka’idojin aminci da aka bai wa dukkan jami’ai da masu son shiga.

Ya bukaci a bi duk shawarwarin tsaro da shirin ya bayar don hana afkuwar lamarin nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *