FG: “A bana ba za a gudanar da bikin ranar samun ‘yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoba”

Gwamnatin tarayya ta ce a bana ba za a gudanar da bikin ranar samun ‘yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoba kamar yadda aka saba yi a dandalin Eagle Square da ke Abuja ba.

Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya ce ranar ‘yancin kai ta wannan shekara za ta kasance “lokacin yin tunani, da kuma nazarin lalubo hanyoyin bunkasa rayuwar al’umma da kuma ci gaba.

Akume ya bayyana hakan ne ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ya fito daga ganawar sirri da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a fadar shugaban kasa.

Sakataren gwamnatin tarayyar wanda ya ki bayyana cikakkun bayanai kan batutuwan da suka tattauna, ya ce tattaunawar na da alaka da shirye-shiryen ranar ‘yancin kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *