Kotu ta ayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano

Kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan Kano ta soke nasarar Abba Kabir Yusuf, a matsayin halastaccen gwamna.

Haka zalika, ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya ci zaɓen da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris ɗin 2023.

Jam’iyyar APC ce ta shigar da ƙara a gaban kotun, tana ƙalubalantar nasarar Abba Kabir.

Kotun ta bayyana wannan hukunci na ranar Laraba ne, ta hanyar manhajar Zoom, cikin wani tsattsauran yanayin matakin tsaro a birnin Kano.

Mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, ita ce shugabar kotun wadda ta jagoranci alƙalan kotun guda uku.

Kotun ta ce ta yanke wannan hukunci ne bisa hujjar cewa an yi aringizon ƙuri’u har 165,633, waɗanda aka gano ba su da sitamfi da kuma kwanan wata a cikin ƙurin Abba Kabir.

Tun farko a watan Maris ɗin 2023, hukumar zaɓen ta ce ɗan takarar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya ci zaɓen ne da ratar ƙuri’a 128,900.

Abba Kabir Yusuf, in ji INEC ya samu ƙuri’u mafi rinjaye da suka kai 1,019,602, inda Nasiru Yusuf Gawuna da ke biye da shi, ya samu ƙuri’a 890,705.

Alƙalan kotun sun umarci hukumar zaɓe ta INEC ta janye shaidar cin zaɓen da ta bai wa Abba Kabir Yusuf, tare da gabatar da ita ga Nasiru Yusuf Gawuna.

Lauyan jam’iyyar NNPP, Bashir Muhammad Tudun Wuzirci bayan fitowa daga kotun, ya ce hukuncin ya zo musu da mamaki, wanda in ji shi bai kamata a ce an yi haka ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *