Tunubu ya samu rakiyar gwamnoni 6 da ministoci 7 zuwa taron majalisar dinkin duniya karo na 78

A yayinda  ake shirin bude taron majalisar dinkin duniya karo na 78 a gobe litinin shugaban kasa Bola Tunubu ya samu rakiyar gwamnoni 6 da ministoci 7,kuma shine karon farko da Tunbu zai halarci irin wannan taro a matsayinsa na shugaban kasa.

Gwamnonin da zasuyi rakiyar shugaban kasa Bola Tunubu sun hada da Hope Uzodinma na jihar  Imo, da gwamna  Umo Eno na jihar  Akwa Ibom, da Mohammed Yahaya na jihar  Gombe da , Uba Sani na jihar Kaduna da gwamna  AbdulRahman AbdulRazak na jihar  Kwara da Seyi Makinde na  Oyo .

Mai magana da yawun shugaban kasa  Ajuri Ngelale,ya tabbatar dacewa  shugaba Tunubu ya kama hanyar tafiya Amruka dan halartar taron na majalisar dinkin duniya a birnin New York.’

Ngelale ya kara dacewa tawagar ta shugaban kasa ta kunshi ministoci guda 7 da suke alaka ta kai tsaye da taron na majalisar dinkin duniya da suka hada da ministan  kula da kasashen waje, Yusuf Maitama Tuggar; da ministan kudi da  tattalin arziki Mr Wale Edun; da ministan Lafiya Farfesa  Mohammed Ali Pate;da Minsitan Tsaro Muhammad Abubakar Badaru;da ministan maadanai Mr , Dele Alake; da ministan jin kai da yaki da talauci  Dr Betta Edu;da kuma ministan masanaantu da kasuwanci da zuba jari Dr Doris Uzoka-Anite.

Sauran mutanan da suke cikin yan tawagar shugaban kasa guda 17 sun hada da shugaban maaikata na fadar shugaban kasa  Femi Gbajabiamila; da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu da shugabar hukumar kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje  Abike Dabiri-Erewa.

Taron na majlaisar dinkin duniya zai maida hankali ne kan magance matsalolin cigaba mai dorewa da sauyin Yanayi a kasashen duniya da hadin kan kasashe  da rikicin da ake fama dashi a wasu kashen duniya da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *