Tinubu ya nada Jamila Bio Ibrahim a matsayin ministar matasa

Shugaban kasar Nijeriya, Alhaji Bola Tinubu, ya amince da nadin Dakta Jamila Bio Ibrahim domin ta kasance ministan kula da harkokin matasa, yayin da za a tsumayi amincewa da nadin nata daga wajen majalisar dattawan Najeriya.

A cewar wata sanarwa dauke da sanya hannun mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Ajuri Ngelale da ya fitar a ranar Lahadi, shugaban ya kuma amince da nadin Ayodele Olawande domin ya kasance karamin ministan harkokin matasa, yayin da shi ma za a jira majalisar dattawa domin tabbatar da zabin da Tinubun ya masa.

Dakta Jamila Bio Ibrahim matashiyar likita ce wacce a baya-bayan nan ta kasance shugabar kungiyar mata ta ‘Progressive Young Women Forum’ (PYWF).

Ta taba yin aiki a matsayin babbar mai taimaka wa gwamnan jihar Kwara kan manufofin cigaba mai daurewa (SDGs).

Shi kuma Ayodele Olawande kwararren masani ne a bangaren cigaban al’umma kuma shugaban matasa ne a jam’iyyar APC.

Aikin da ya yi a baya-bayan nan kafin wannan nadin shi ne ya kasance babban mashawarci ga shugaban kasa kan kirkire-kirkiren zamani daga shekarar 2019 zuwa 2023.

A kan hakan, shugaban kasa, Bola Tinubu ya bukaci wadanda aka nadan da su yi amfani da azamarsu, kokarinsu, hikimarsu, dabararsu wajen kyautata rayukan matasan Nijeriya yayin da suke gudanar da ayyukansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *