“Har yanzu wasu ‘yan Najeriya kusan 100 su na makale a Sudan”

Rahotanni daga Sudan sun ce, har yanzu wasu ‘yan Najeriya kusan dari su na can a makale, su na jiran a kwaso su zuwa gida.

Sun ce sun kasa ficewa daga kasar sakamakon yakin da ake yi a Sudan.

‘Yan Najeriyan, sun ce su na cikin mawuyacin hali sakamakon matsalolin karancin abinci da ruwan sha da kudi da sauran kayan bukatun rayuwar yau da kullum.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta yi alkawarin za ta kwashe su, ta mayar da su gida, amma yanzu haka an yi watanni biyu su na jira, kuma babu wani labari game da hakan.

Yanzu haka akwai ‘yan Nijeriya 85 wadanda suka kunshi maza 60 da mata 25 da kuma kananan yara da suka makale a garin Bar-Sudan na gabar tekun Bahar Maliya a gefen kasar su na can su na dakon a mayar da su gida Nijeriya sakamakon yakin da ake tafkawa tsakanin bangarorin sojin kasar.

Ya ce shi da sauran mutane su na zaman jiran aje  a kwashesu amma har yanzu ba a turo ba kuma a yanzu sun shafe tsawon watan biyu cif-cif da faruwar alamarin.

Akwai kungiyoyin agaji da ke taimaka mu su da abinci amma sau daya su ke kawo wa a rana kuma kwantaragin aikinsu ya zo karshe a cewarsa. Sun kuma yi ikirarin cewa tafiya a kasa na cike da hadari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *