An kai karar Tinubu a gaban kotu bisa gazawarsa wajen hana wasu ministocinsa guda takwas

An kai karar shugaban kasa Bola Tinubu a gaban kotu bisa gazawarsa wajen hana wasu ministocinsa guda takwas, da suka haɗa da Nyesom Wike da David Umahi karbar kuɗaɗen fansho a matsayin tsaffin gwamnoni.

Ƙungiyar nan ta  SERAP mai rajin yaki da cin hanci da rashawa itace ta shigar da ƙarar tare da sanya wasu ministoci shida matsayin wadanda ake tuhuma a cikin ƙarar.

Tunda farko SERAP ta nemi shugaban kasa Tunubu da ya hana wasu tsofaffin gwamnoni da ya nada mukamin ministoci karbar kudaden fansho a jihohinsu,saidai rahotanni na nuni dacewa kiran na SERAP bai samu shiga ba,shiyasa ta garzaya zuwa kotu.

 Tsofaffin ministocin da ake neman shugaban kasa Tunubu ya hanasu karbar Fansho sun hada da  Badaru Abubakar, na jihar Jigawa da Bello Matawalle, na  Zamfara da Adegboyega Oyetola, na Osun da Simon Lalong, na Plateau da Atiku Bagudu na Kebbi da Ibrahim Geidam na jihar Yobe sai Nyesom Wike na Rivers da  , David Umahi daga jihar Ebonyi.

Ƙungiyar ta bayyana cewa gazawar da Shugaba Tinubu ya yi na bai wa tsofaffin gwamnonin da ke riƙe da muƙamin ministoci su daina karbar kuɗaɗen fansho, cin zarafi ne ga rantsuwar da ya yi wajen kama mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *