Tinubu zai bar Abuja zuwa Amurka domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) 2023

Shugaba Bola Tinubu a ranar Lahadi ne zai bar Abuja, domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) 2023, wanda za a gudanar a birnin New York na kasar Amurka.

Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Ajuri Ngelale,shi ne wanda ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a.

Ya ce shugaban, baya ga babban taron majalisar dinkin duniya, zai gana da manyan masu ruwa da tsaki a harkokin tattalin arziki a duniya.

“Baya ga alkawurran da zai yi a zauren Majalisar, baya ga aikin shigar da tawagar Najeriya a Majalisar, akwai wasu ayyuka masu matukar muhimmanci da za su yi tasiri a kan tattalin arzikin Najeriya.

“Bayan nasarar da shugaban ya yi zuwa New Delhi don halartar taron G-20, da kuma dimbin jarin da ya samu ya jawowa Najeriya cikin kankanin lokaci, zai ci gaba kan tattalin arzikinsa da yunkurin diflomasiyya don jawo hannun jarin kasashen waje kai tsaye zuwa cikin kasar,” in ji Ngelale.

Ya tabbatar da cewa shugaban zai yi ganawa da manyan shuwagabannin zartarwa da shugabannin kamfanoni na kasa da kasa, ciki har da Brad Smith, shugaban Kamfanin Microsoft a duk duniya; Sir Nick Clegg, Shugaban Meta Technologies; da shugabannin General Electric da Exxon Mobil.

A cewarsa, ayyukan da shugaban zai yi zai hada da ganawa da shugabannin kasashen Amurka, Comoros, Afirka ta Kudu, da kuma kungiyar Tarayyar Turai.

Tinubu zai kuma gana da firaministan Spain da Netherlands, Sarkin Jordan, da shugabannin Aljeriya da Brazil.

“Har yanzu yana da kuzari. Akwai wadanda har yanzu za a kara da su, amma ya kamata a ce nan da ‘yan kwanaki kadan a birnin New York, tabbas mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kasance daya daga cikin masu fafutuka kuma daya daga cikin shugabannin kasashen da ake nema ruwa a jallo dangane da yadda yake tafiyar da harkokin bangarorin biyu da na bangarori daban-daban,” in ji Ngelale.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *