Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada aniyarsa na samar da kyakywan rayuwa ga alummar wannan kasa, yana mai bayyana ƴan Najeriya da cewa mutane ne masu ƙwazo, da babu wani dalili da zai sanya su zauna cikin talauci.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar wasu dattawan ƙasar, da suka haɗar da jagororin jam’iyyun APC da PDP, a fadar shugaban ƙasa.
Shugaban Tinubu ya ƙara da cewa duk da dai cewar a yanzu alummar kasa na fuskantar tsanani, amma al’amurran zasu inganta, tare da bayyana kwarin gwiwar da ya ke da ita akan cimma muradan gwamnatin sa na samar da kyakyawar kasa.