Aƙalla mutum 586 ne aka kashe tare da sace 369 a watan Agusta a fadin Najeriya, kamar yadda binciken cibiyar nazarin harkokin tsaro ta Beacon Intel ya bayyana.
Cikin rahoton da cibiyar ta fitar ranar Alhamis, ta ce an samu kashe-kashe a jihohin Najeriya 34, da kuma birnin tarayya Abuja, yayin da aka samu sace-sacen mutane a jihohi 24 na ƙasar.
A cewar rahoton, an kashe mutum 41 sakamakon ƙwanton ɓauna da aka yi musu a wurare daban-daban, sai kuma mutum 256 da aka kashe ta hanyar musayar wuta, sai mutum 69 da suka mutu a lokacin kai samame, sai dai sauran 118 ba a san musabbabin mutuwarsu ba, kamar yadda rahoton ya bayyana.
Rahoton ya kuma bayyana cewa an kashe mutum 89 a lokacin kai hare-hare, yayin da 15 suka mutu a lokacin da ake tsare da su.
Jihohi uku da lamarin ya fi shafa su ne, Borno inda aka kashe mutum 252, sai Filato mai mutum 31 sai jihar Neja da aka kashe mutum 26.