“Muna ci gaba da bincike kan mutane da aka jikkata sanadin harbin bindiga a kasuwar Garki”. – DSS

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta ce tana ci gaba da bincike, kuma za ta riƙa fitar da bayanai lokaci-lokaci, game da batun wasu mutane da aka jikkata sanadin harbin bindiga a kasuwar Garki.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, hukumar ta ce mutanen da aka jikkata ranar 7 ga watan Satumba a Abuja, sun cancanci samun tallafi da kuma adalci.

DSS ta ce tuni ta kafa kwamiti a cikin gida don yin bincike, kuma jami’anta sun ziyarci mutum biyu da aka jikkata, waɗanda ke kwance suna jinya a asibitoci daban-daban.

Ba a dai saba jin hukumar DSS ta fito bainar jama’a, aƙalla tana nuna nadama a kan irin wannan lamari na zafin hannu da aka zargi wani jami’inta da aikatawa a kan wani ɗan ƙasa ba.

Sanarwar ta ce hukumar tana tuntuɓar dangin waɗanda lamarin ya ritsa da su, kuma za ta ci gaba da bibiyar halin da lafiyarsu take ciki.

Tuni da a cewarta, ta yi alƙawarin biyan kuɗin magani har ma ta ajiye wani ɓangare na kuɗin da aka nema, sannan a yayin ziyarar marasa lafiyan da jami’anta suka kai, hukumar ta bayyana aniyar mayar da su zuwa wani asibitinta da ke Abuja, don samun kulawa mafi inganci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *