Iyaye sun koka kan yajin aikin da ake yi a makarantun Gwamnati na Abuja

A Jawabansu daban-daban, iyaye a karamar hukumar Gwagwalada babban birnin Tarayya Abuja sun koka kan yajin aikin da ake yi a Makarantun Gwamnati ba kakkautawa, inda suka ce yana tauye wa ‘ya’yansu ‘yancin yin karatu.

Iyayen a wata Tattaunawa daban-daban da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN yayi da su a ranar Juma’a a Abuja sun bayyana yajin aikin a matsayin abin takaici kuma abin kunya ga ɓangaren ilimi.

NAN ta ruwaito cewa kungiyar malamai ta Najeriya NUT reshen Babban Birnin Tarayya a ranar Litinin ta umurci mambobinta na kananan hukumomi shida da su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

Kungiyar ta bada wannan umarni ne a cikin wata sanarwar da ta fitar a ƙarshen taronta na gaggawa na majalisar zartarwar Kungiyar ta jiha SWEC da ta gudanar a Gwagwalada.

Sanarwar da Shugaban NUT na Jihar Stephen Knabayi da Sakatariyar Misis Margaret Jethro suka sanya wa hannu, sun ce an fara yajin aikin ne a ranar 11 ga watan Satumba.

Sun yi zargin cewa Gwamnati ta gaza biyan bukatunsu da suka hada da rashin aiwatar da biyan bashin ƙarin girma, rashin inganta aikin malaman, da rashin aiwatar da ƙarin kuɗaɗe na shekara shekara da dai sauransu.

Christopher Onah wani mai sana’a kuma mahaifin ‘ya’ya uku ya ce abin takaici ne ganin ‘ya’yansa na zaune a gida yayin da wasu ke shagaltuwa da karatun su a sauran Makarantu masu zaman kansu

Mista Onah ya ce kudin da yake samu ya sa ya kasa kai ‘ya’yansa makaranta mai zaman kanta inda za su samu ilimi mai inganci.

“Ina matukar bakin ciki da rashin jin dadin ganin ‘ya’yana a gida yayin da ƴan’uwansu ɗalibai ke makaranta, hakan na iya sa su tsunduma cikin ayyukan da suka saba wa zamantakewa domin ba su shagaltu da ayyukan masu ma’ana ba”, inji shi.

“Ina rokon Gwamnati da ta duba halin da yaran nan ke ciki domin ‘ya’yanmu su iya zuwa makaranta tunda wannan ne kawai zabin da nake da shi.

Ita ma Aishat Sule ‘yar karamar ‘yar kasuwa mai yara biyar ta ce ta ji daɗi da taga cewa hutu ya kare, bayan nan ne kawai ta samu labarin cewa malaman firamare na LEA na yajin aiki.

Kuma waɗannan yara za su rubuta jarrabawar kammala Firamare ne tare da takwarorinsu na makarantu masu zaman kansu, to ta yaya za su iya kammala karatun zangon yayin da ake yajin aiki a Makarantun Gwamnati? ya kamata su kasance mafi kyawun makarantu domin hakan zai hana mutane zuwa
Makarantu masu zaman kansu amma da wannan yajin aikin hakan ba zai samu ba.

Sai suka roƙi Gwamnati da ta taimaki talakawa da baiwa ‘ya’yanmu ilimi mai inganci,” inji ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *