Gwamnatin Tarayya ta bukaci gwamnatocin jihohi daban-daban dasu maida hankali kan harkar noma

Gwamnatin Tarayya ta bukaci gwamnatocin Jihohi daban-daban dasu maida hankali kan harkar noma don ciyar da tattalin arzikin kasarnan gaba tare da magance kalubalen  talauci a tsakanin al’umma.

Da yake jawabi a wajen taro karo na 22 na Kwamitin Tsare Tsare na Kasa a Osogbo, Babban Sakatare na dindindin na Ma’aikatar Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Nebeolisa Anako yace mayar da hankali kan sauya tsarin samar da abinci zai iya yakar matsalar rashin abinci mai gina jiki da kuma inganta samar da ayyukan yi ga matasa

A cewarsa, mayar da hankali kan tsarin darajar aikin gona zai iya inganta tattalin arzikin halittu tare da inganta darajar abinci mai gina jiki ta hanyar maida hankali kan hanyar sauya abinci da za’a magance tabarbarewar cigaban mazauna karkara.

Taron mai taken Mahimmancin Maido da Najeriya Kan Tafarkin Tattalin Arziki Mai Dorewa da cigaba,zai mayar da hankali kan magance wahalhalun da jama’a ke ciki sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin kasar tayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *