Gwamnan Legas ya rantsar da kwamishinoni da masu ba shi shawara na musamman 38

Gwamnan Jihar Legas Mista Babajide Sanwo Olu a ranar Laraba ya rantsar da kwamishinoni 38 da masu ba da shawara na musamman.

Bikin rantsarwar wanda aka gudanar a dakin taro na Adeyemi Bero Alausa Ikeja ya nuna alamar ƙaddamar da Majalisar abokan aikin Gwamnan a karo na biyu a kan karagar mulki.

Majalisar Dokokin Jihar Legas bayan wasu korafe-korafe sun tabbatar da sunayen mutane 38 da za a naɗa a matsayin ƴan Majalisar Gwamnan Jihar inda aka tabbatar da Tantance na karshe Tolani Akibu kasa da sa’o’i 24 kafin rantsar da shi.

Mambobin Majalisar zartarwar Jihar da aka rantsar sune Mista Layode Ibrahim da Mr Mobolaji Ogunlende da Dr Dolapo Fasawe da Bola Olumegbon da Mr. Idris Aregbe da Msr. Abisola Olusanya da Mr. Moruf Fatai da Mr. Kayode Bolaji Roberts da Injiniya Abiola Olowu da Mrs. Toke Benson Awoyinka da Dr. Oreoluwa Finnih Awokoya da Mr. Yakub Alebio (SAN) da Mr. Lawal Pedro
da Mr. Tunbosun Alake.

Sauran sun hada da Mr Gbenga Oyerinde Dr Adekunle Olayinka Dr Jide Babatunde Mr Afolabi Ayantayo Mr Tokunbo Wahab Mr Olakunle Rotimi Akodu Mr Jamiu Alli Balogun Mr Abdulkabir Ogungbo Dr Afolabi Tajudeen Mr Oluwaseun Osiyemi da kuma Farfesa Akin Abayomi.

Sauran sun hada da Dr Oluwarotimi Fashola Mrs Folashade Ambrose Medem Mrs Akinyemi Ajigbotafe Mrs Bolaji Dada Mrs Barakat Bakare Mr Olugbenga Omotoso Mr Mosopefoluwa George Dr Yekini Agbaje Dr Olumide Oluyinka Mr Abayomi Oluyomi Dr Iyabode Ayoola Sola Giwa da Tolani Akibu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *