Gwamnan Kano ya dakatar da shugaban hukumar kula da noma na jihar.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da shugaban hukumar kula da noma na Kano (KASCO), Tukur Dayyabu Minjibir, bisa rashin da’a da karkatar da kudade.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Laraba, mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Sanarwar ta ce matakin wani bangare ne na kudirin gwamnati na yaki da duk wani nau’in cin hanci da rashawa.

A cewar sanarwar, “Gwamnan ya bayar da umarnin dakatar da shi ne a wata takarda mai dauke da kwanan watan 12 ga watan Satumba shekarar 2023, wanda sakataren gwamnatin jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi ya mika.”

Ya ce an dakatar da Manajan Darakta ne bisa zargin hannu a sayar da hatsi na gwamnatin jihar da aka bayar ga talakawa.

An umurci Dayyabu da ya mika al’amuran hukumar ga babban jami’i a hukumar har sai an kammala bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *