“Bambance-bambancen harsuna da ake dashi a Nijeriya, shine musabbabin karfin kasar” – Remi Tinubu

Uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu, ta tabbatar da cewa bambance-bambancen harsuna da ake dashi a Nijeriya, shine musabbabin karfin kasar.

Tace ta hanyar rayuwa cikin kwanciyar hankali da soyayya ne za’a iya aiwatar da Basira da Hikimar da ubangiji ya baiwa dan adam

A cewar wata sanarwa da mai taimaka mata kan harkokin yada labarai, Busola Kukoyi ya fitar, yace, Remi Tinubu, ta yi wannan furucin ne a wajen rabon kayan agaji da sake tsugunar da iyalai 500 da rikicin kabilanci ya shafa a kananan hukumomi shida na jihar Filato.

Anasa jawabin, gwamnan jihar Filato, Barr. Caleb Mutfwang, ya yabawa uwargidan shugaban kasar

Kimanin iyalai 500 da aka zabo daga kananan hukumomin Mangu, Riyom, Barkin Lado, Bassa, Bokos da Jos ta Kudu na jihar sun samu Naira miliyan daya  domin su koma yankunansu su sake gina gidajensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *