Akpabio ya yabawa Tinubu kan jajircewarsa wajen magance matsalar biza da Daular Larabawa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan abinda ya kira, hazaka da jajircewarsa wajen magance matsalar biza da Daular Larabawa.

Akpabio wanda ya bayyana matakin a matsayin kokari na zamantakewa da siyasa, ya bayyana cewa, hazaka ne shugaban kasa ya maido da huldar diflomasiyya tsakanin Najeriya da hadadiyyar daular larabawa, la’akari da asarar tattalin arzikin da kasashen biyu suka yi yayinda rashin jituwa ya shiga tsakaninsu.

Cikin wata sanarwa  ta hannun mai bashi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Eseme Eyiboh, yace warware rikicin kasashen biyu cikin lumana, na kan hanyar samun riba mai yawa daga alakar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *