“Najeriya na bukatar Naira tiriliyan 21 don cike gibin gidaje yadda ya kamata” – Shettima

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana cewa Najeriya na bukatar Naira tiriliyan 21 don cike gibin gidaje yadda ya kamata, duk da kokarin da ake yi a matakai uku na gwamnati.

Shettima ya bayyana haka ne a Sokoto a wajen kaddamar da ginin rukunin gidaje 500 da gwamnatin jihar ta yi.

Mataimakin shugaban kasar wanda ya yabawa gwamna Ahmed Aliyu bisa kokarin da yake yi na magance bukatun gidaje na al’ummar jihar sa, ya bayyana cewa gibin gidaje a Najeriya ya kasance babban kalubale.

Tun da farko, Gwamnan ya bayyana cewa gidajen na ma’aikatan gwamnati ne kuma za a sayar musu da su idan an kammala su bisa farashi mai rahusa. Taron wanda ya kasance na cika kwanaki 100 na farko a kan karagar mulki da gwamnatin ta yi, ya samu halartar Sanata Aliyu Wamakko, Ministan Noma da samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *