Indiya ta mika wa Brazil shugabancin G20 a hukumance

Indiya ta mika wa Brazil shugabancin G20 a hukumance a bikin rufe taron shekara-shekara da aka yi a New Delhi a karshen mako.

Firayim Ministan Indiya Narendra Modi ya kammala mika mulki ne ta hanyar mika ragamar shugabancin ga shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva.

Indiya ce ke shugabancin G20 tun ranar 1 ga watan Disamba, lokacin da ta karbi ragamar mulki daga Indonesia, kuma za ta ci gaba da rike mukamin har zuwa ranar 30 ga Nuwamba.

A yayin taron na kwanaki biyu, kungiyar ta amince da sanarwar bai daya, wadda ta dauki alkawura kan batutuwa da dama, da suka hada da samar da abinci da makamashi, da sauyin yanayi, da kuma rangwamen bashi a duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *