Biden ya yaba wa Tinubu kan ƙarfin shugabanci a matsayinsa na shugaban Ecowas.

Shugaban Amurka Joe Biden ya yaba wa takwaransa na Najeriya Bola Tinubu kan ƙarfin shugabanci a matsayinsa na shugaban Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas.

Mista Biden ya jinjina wa Tinubu a ƙoƙarinsa martaba tare da kare dimokraɗiyya a jamhuriyar Nijar da yankin Afirka ta Yamma.

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa Shugaban na Amurka ya gana da Tinubu a gefen taron ƙungiyar G-20 ta kasashe masu karfin masana’antu da aka gudanar a birnin Derkhi na kasar Indiya.

An yi ganarwa ne domin jaddada goyon bayan Amurka ga Najeriya, kamar yadda ofishin jakadancin Amurkan a Najeriya ya bayana.

Ta kara da cewa ”gayyatar da aka yi wa Najeriya zuwa taron G-20 alama ce irin martabar da ƙasar ke da ita a idon duniya, a matsayinta na giwar dimokraɗiyya da tattalin arziki a duniya”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *