Koda an gyara matatun man fetur ɗin Najeriya, mai ba zai sauko ƙasa da 200 ba – Dillalai man fetur

Kungiyar manyan dillalan man fetur ta Najeriya ta ce ba zai yiwu farashin man fetur ya yi kasa da Naira 200 ba, ko da an gyara matatun mai.

Kungiyar ta lura da hakan ne biyo bayan wani rahoto da aka buga kwanan nan, inda kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya ta ce farashin man fetur zai fadi kasa da Naira 200 kan kowace lita idan matatun sun sake fara aiki.

Shugaban kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya reshen jihar Ribas Joseph Obele, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta tabbatar an gyara matatun man kasar kamar yadda aka tsara.

Ya ce, “Har sai matatun man kasarmu sun fara aiki, farashin mai zai ci gaba da karuwa saboda sauyin yanayi na kasa da kasa. Amma idan matatun mu suka yi aiki, ‘yan Najeriya za su sayi mai kasa da Naira 200 kan kowace lita.

“Rashin dala ya sa masu shigo da man fetur ke da wuya su ci gaba da shigo da su daga waje. Kimanin makonni biyu ke nan, sarkar rarraba man fetur ta fuskanci tashin hankali. Wannan ya bayyana a kan tashar saye da sayar da mai na NNPC.”

Da yake zantawa da jaridar babban jami’in gudanarwar kuma tsohon shugaban kungiyar ‘yan kasuwar man fetur ta Najeriya, Tunji Oyebanji, ya ce canjin dala na shafar farashin man fetur.

Ya kuma ce farashin danyen mai a kasuwannin duniya na kan hauhawa saboda yawan bukatu da rage da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta yi.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya mayar da martani ga hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da ta tabbatar da zaɓen da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Wata sanarwa da ya sanya wa hannu, wacce ofishin yada labaransa ya fitar, ta bayyana hukuncin kotun sauraron ƙararraki a matsayin nasara ga dimokuradiyya da bin doka da oda

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *