Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas, Alhamis, ta dage ci gaba da zama har zuwa ranar 9 ga watan Oktoba, domin sauraren karar da lauya Nkereuwem Mark Anana ya shigar a madadin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Abdulrasheed da aka dakatar, a kan Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS) da wasu mutane biyu.
Shugaban EFCC da aka dakatar, Bawa yana tsare tun ranar 14 ga watan Yunin 2023, lokacin da jami’an tsaron farin kaya (DSS) suka kama shi. Ba a gurfanar da shi a kotu ko kuma a ba da shi beli ba.
Lauyan ya maka Darakta-Janar na DSS, DSS da Atoni-Janar na Tarayya (AGF) a gaban Kotu, bisa laifin tauye hakkin Shugaban Hukumar EFCC, a wata kara mai lamba FHC/L/CS/. 1631/2023.
Mai shari’a Akintayo Aluko ya sanya ranar 9 ga watan Oktoba domin sauraren karar, biyo bayan bukatar da Anana ya gabatar, inda ya shaidawa kotun cewa yana bukatar ya mayar da martani kan matakin farko da Darakta Janar na DSS ya shigar.
A cikin karar, Anana, tsohon mai shigar da kara na EFCC ya nemi “Kudin Naira miliyan 100, a matsayin diyya ga wadanda ake kara na daya da na biyu.”
Sai dai hukumar ta DSS da babban daraktan ta, a matakin farko da lauyansu, Mista Michael Bajela ya shigar, sun bukaci kotun da ta biya lauyan naira miliyan 200 a matsayin diyya ta gaba daya.