“Akwai yiyuwar samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu jihohin Najeriya 20” – NiMet

Hukumar kula da hasashen yanayi ta kasa NiMet ta tabbatar da cewa akwai yiyuwar samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu jihohin Najeriya 20 ciki harda Kano.

Nimet tace nan da awanni 48 daga daren jiya za,a samu mamakon ruwan saman ne bayan wani rahoto data samu na hasashen ruwan saman.

Mamakon ruwan saman da ake sa ran farawa a cikin karshen makon nan daga Ranar Asabar ana sa ran zai stafe kwanaki uku anayinsa.

Bayan Kano ana sa ran samun ruwan saman a  Legas, Ogun da Adamawa ,da Delta da Bayelsa da Akwa Ibom da Zamfara da Yobe da Benue da Sokoto da Jigawa da Katsina da Cross River .

Sai kuma inda za,a samu matsakaicin ruwa a jihohin Borno da Bauchi da Kaduna da Naija daga Gobe Asabar.

Kazalika akwai yiyuwar samun ambaliyar ruwa a wannan kawanaki uku da za,a shafe ana ruwan sama a  Ribas, Delta, Bayelsa, Akwa Ibom da kuma Kuros Riba a yankin kudancin Najeriya.

A Arewa kuma NiMet tace akwai  Yobe,da  Binuwai,da  Jigawa, da Kano, da Katsina, Zamfara da Sakkwato Neja, Borno, Bauchi da Kaduna su na cikin inda hukumar ta ke ganin za ayi ruwa kadan ko kuma ba za a samu ba gaba daya a ‘yan kwanakin nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *