Tinubu yayi maraba da hukuncin da kotu ta zartar da yammacin ranar Laraba

Shuagaban kasa  Bola Ahmed Tinubu yayi maraba da hukuncin da kotun sauraron karar zaben shugaban kasa ta zartar da yammacin ranar Laraba

Shugaban anata bakin Hadiminsa a kafafen yada labarai , Ajuri Ngelale, ya tabbatar da cewar zai maida hankali wajen cika alkawuran daya dauka na kawo zaman lafiya da cigaba a kasa

Hukuncin ya kara tabbatar da jajircewa da shirin shugaba Tinubu na hidimtawa daukacin ‘yan Najeriya ba tare da nuna wani bambanci ba.

A jawabinsa, Ajuri Ngelale ya bayyana cewar shugaba Tinubu ya yabawa  Mai shari’a Haruna Tsammani da sauran Alkalai kan yadda suka fassara doka.

Shugaban kasar ya kuma  ce hukuncin korafin zaben ya nuna yadda tsarin shari’ar Najeriya ya cigaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *