Ku taya mu da addu’a domin samun nasara akan yan ta’adda – Ministan Tsaro

Ministan tsaro, Alhaji Mohammed Badaru, ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yin addu’o’in kawo karshen matsalolin tsaro a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Badaru ya yi wannan kiran ne ranar Alhamis a Abuja lokacin da ya karbi bakuncin tawagar yan asalin jahar Jigawa karkashin jagorancin gwamnan jihar, Malam Umar Namadi.

Ministan tsaron, ya ce duk da cewa aikin da ke gabansu na da yawa, amma sun kuduri aniyar shawo kan kalubalen.

Don haka Badaru ya tashi tsaye wajen neman goyon bayan daukacin ‘yan Najeriya ciki har da addu’o’insu domin ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.

Tun da farko gwamnan jihar Jigawa wanda ya jagoranci sarakunan gargajiya da malaman addini da ‘yan kasuwa da masu rike da mukaman gwamnati daga jihar ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin taya ministan murna tare da ba shi tabbacin goyon bayansu a kowane lokaci.

Ba wai don taya murna ba ne, har ma a yi muku addu’a. Mun san yadda ka yi nasara a matsayinka na gwamnan jiharmu, muna kuma yi maka addu’ar samun nasara ko ma fiye da haka a wannan sabon aikin na Ministan Tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *