Kotu ta tabbatar da cewa Bola Ahmad Tinubu ne ya lashe sakamakon zaben 2023

Kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban Kasa ta tabbatar da cewa Bola Ahmad Tinubu ne ya lashe sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun data gabata.

Alkalan kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Haruna Tsammani ne ya tabbatar da haka bayan yanke hukuncin karshe a zaman kotun na ranar Laraba.

Kotun ta kuma ce Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) tayi daidai data ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben.

A cewar kotun, wadanda suka shigar da karar sun gaza gabatar da gamsassun hujjojin da zasu  tabbatar da da’awarsu.

Mai Shari’a Tsammani yace, “Hujjojin da masu shigar da kara suka gabatar ba kwarara bane

Kotun ta kuma yi watsi da hujjoji 37 da shaidun suka gabatar a gabanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *