Buhari ya bayyana farin cikinsa da hukuncin da kotu ta yanke na tabbatar da nasar Tinubu da Shettima a zaben 2023

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana farin cikinsa da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke na tabbatar da nasarar jam’iyyar APC da dan takararta, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

A wani jawabi daya fitar ta bakin kakakinsa, Garba Shehu, yace nasarar Bola Tinubu da Kashim Shettima nasara ce ga daukakin ‘yan kasar nan

Muhammadu Buhari yayi magana ne jim kadan bayan kotu ta tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa

Tsohon shugaban kasar yace PEPC ta rubuta tarihi ta hanyar yin watsi da tursasawa da duk wani nau’i na son zuciya don tabbatar da adalci bisa doka ga yawancin ‘yan kasar da burinsu shine a mutunta zabin da suka yi.

Tsohon shugaban kasar ya kuma bayyana jin dadinsa ga daukacin ‘yan kasa kan yadda suke wanzar da zaman lafiya a tsawon wannan lokaci tare da addu’ar samun cigaba a gwamnatin APC.

Ya kuma bukaci yan Najeriya dasu tabbatar sun goyi bayan wannan gwamnatin wajen ganin an kaiga samun nasarar gudanar da aiyuka na alheri da aka soma gudanarwa cikin dan kankanin lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *