Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Cif Olabode George, ya nuna damuwa kan rawar da bangaren shari’a ke takawa wajen tantance wadanda suka lashe zabe a Najeriya.
Hakan na zuwa ne a yayin da ya shawarci bangaren shari’a da su guji tauye hakkin jama’a na tantance wadanda suka yi nasara a zabuka.
Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai da ya gudanar a ofishinsa da ke Ikoyi bayan da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta bayyana a Abuja cewa za ta yanke hukuncin korafin zaben shugaban kasa a gobe Laraba.
Kotun, a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Litinin, ta bayyana cewa a gobe Laraba ne za ta yanke hukunci kan karar da ta shigar da ke kalubalantar ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023 da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta yi.
PUNCH