Obasanjo: “A iya sanin Buhari da na yi, ban san ya iya yin bushasha da kuɗi fiye da yadda nake tsammani ba”.

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa a iya sanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi, bai san ya iya yin bushasha da kuɗi fiye da yadda ake tsammani ba.

A hira da da yayi da ‘yan Jarida, Obasanjo ya ce zai yi wuya kasashen da ke bin Najeriya bashin kuɗi su yafe mata kamar yadda aka yi a lokacin mulkin sa, ganin yadda aka rika kashe kuɗi na babu gaira babu dalili a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Buhari.

Da yake magana game da matatun man kasar nan, Obasanjo ya ce wahalar da kai za a yi ta yi idan ya kasance har yanzu maganar gyaran su ake yi.

A cewarsa matatun man ba za su taba gyaruwa ba matukar dai suna karkashin kulawar gwamnati ne, inda yace ‘yan kasuwa ne kawai za su iya rike su, su gyara su sannan su tayar da su su fara aiki.

Obasanjo yace a lokacin mulkinsa ya mayar da matatun hannun ‘yan kasuwa, amma gwamnatin da ta gaje shi ta maida su karkashin kulawar gwamnati, yana mai jaddada cewa gwamnati ba ta iya rike su ba a yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *