Naira biliyan 2 FG ta bamu – Gwamnan Bauchi

Gwamnatin Jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Sanata Bala Muhammad ta ce naira biliyan biyu gwamnatin tarayya ta aike mata dashi kudin tallafi.

Idan ba a mance ba gwamnatin tarayya ta yi alkawarin aikewa kowace jiha garin kuɗi naira biliyan biyar don fitar da yan jiha daga cikin radadin da janye tallafin man fetur ya haifar.

Toh sai dai a wata hira a ranar Litinin gwamnatin ta bakin kwamishinar harkoƙin jinƙai da kula da bala’o”i na Jihar Hajiya Hajara Yakubu Wanka ta ce naira biliyan biyu gwamnatin ta aike mata mata dashi inda kuma tuni ta yi kasagin yadda za a yi amfani da shi.

Ta ce gwamnatin za ta yi amfani da naira miliyan 680 wajen magance matsalar kuɗin hutu ma’aikata, yayin da miliyan 500 kuma za a ɓatar da shi wajen biyan giratuti.

Kazalika kuma naira miliyan 325 an wareshi don rabawa ga al’umma inda miliyan 76 kuma zai zo ne zuwa ga hannun mata da matasa.

A bangaren giratutin ƙananan hukumomi an ware naira miliyan 300 don rage musu raɗaɗi yayin da ma’aikatan wuci gadi na kiwon lafiya kuma aka ware musu naira miliyan 60 don sanya su cikin tsarin.

Bugu da ƙari gwamnatin jihar ta ce su ma ɗalibai daga ƙananan hukumomin Bauchi da Ningi da Misau da kuma Katagum ba za a yi banda su ba inda su ma tuni aka ware musu wani kaso mai tsoka don sayen motocin ɗalibai.

Da ma dai tun da farko ne gwamnatin ta ce za ta kara naira biliyan biyu kan kudin tallafin da gwamnatin tarayyar ta ware.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *