DSS ta ce ta gano shirin da wasu mutane ke yi na gudanar da zanga-zangar tashin hankali a faɗin ƙasa

Rundunar tsaro ta DSS ta ce ta gano shirin da wasu mutane ke yi na gudanar da zanga-zangar tashin hankali a faɗin ƙasa domin nuna gazawar gwamnatin tarayya da kuma jami’an tsaro na magance batun matsin rayuwa da mutane ke ciki.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun DSS ɗin Peter Afunanya ya fitar, ta ce an samu bayanan sirri da ke nuna cewa mutane da ke shirin yin zanga-zangar sun kunshi wasu ƴan siyasa da ke haɗa kan shugabannin ɗailbai, kungiyoyin kabilu da matasa da kuma fusatattun kungiyoyi.

DSS ta ce tana sanya ido kan shugabannin kungiyoyin domin dakatar da su daga jefa ƙasar cikin zaman rashin doka.

Hukumar ta kuma shawarci shugabannin Jami’o’i da sauran makarantu da su ja hankalin ɗalibansu daga shiga cikin abubuwan da za su janyo rashin zaman lafiya.

Har ila yau, DSS ɗin ta buƙaci iyaye da su riƙa yi wa ‘ya’yansu nasiha na su guji shiga cikin abin da zai karya doka da oda.

Hukumar ta sha alwashin kama duk wanda ya yi ƙoƙarin tayar da zaune tsaye a faɗin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *