“‘Yan bindiga dake aiki a Arewa maso Yammana kasarnan na daukar wasu dabarun ‘yan ta’adda”. – Lagbaja

Babban hafsan sojin kasarnan, Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, yace ‘yan bindiga dake aiki a shiyyar Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya na kasarnan na daukar wasu dabarun ‘yan ta’adda.

Babban hafsan sojin yayi wannan jawabi ne a lokacin daya karbi bakuncin Mataimakin Sakatare Janar na Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da ta’addanci, Vladimir Voronkov, a ofishinsa da ke Abuja

Lagbaja yace rundunar a shirye take ta hada kai da kungiyar domin dawo da zaman lafiya a sassan kasarnan da ke fama da rikici.

Lagbaja ya nemi goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da sauran sassan kungiyar kan shirin kawar da yan ta’adda.

Ya kara da cewar rundunar sojojin Najeriya na saran goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya dama sauran sassan Majalisar Dinkin Duniya kan shirin.

Anasa bangaren, Voronkov yayi alkawarin cewar kungiyarsa zata gina Najeriya wajen ganowa,tare da gudanar da bincike da kuma hukunta masu aikata laifukan da suka shafi ta’addanci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *