Shettima: “Rashin shugabanci nada alaka kai tsaye da yawaitar ‘yan fashi da garkuwa da mutane a shiyyar arewa maso yamma”.

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima yace rashin shugabanci nada alaka kai tsaye da yawaitar ‘yan fashi da garkuwa da mutane a shiyyar arewa maso yamma.

Shettima yayi wannan jawabi ne a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar hadin kan ‘yan kasuwa, masana’antu, ma’adanai, da noma na jihohin Arewa, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Mataimakin shugaban kasar yace daidaita yanayin mulki a al’amuran arewa ya zama wajibi domin a cigaban yankin.

Shettima yace masu ruwa da tsaki a yankin arewa baki daya dole ne su sake duba yadda al’amuran yankin suke, sannan su fito da matakai na sake farfado da al’ummarsu.

Ya kara da cewar yana da matukar muhimmanci ga arewa ta fara shirin sake fasalin yankin da kuma sake farfado dashi domin a samu ci gaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *