Babu batun ɗaga kafa ko baiwa sojojin Nijar dogon lokaci kafin mayar da ƙasar kan turbar dimokuraɗiyya – ECOWAS

Ƙungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka, Ecowas ta jadadda cewa babu batun ɗaga kafa ko baiwa sojojin Nijar dogon lokaci kafin mayar da ƙasar kan turbar dimokuraɗiyya.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, Ecowas tace anja hankalinta kan wasu rahotanni dake cewa ta bada shawarar wa’adin miƙa mulki, wanda kuma wannan labari ba daga wajenta ya fito ba.

Ecowas tace rahotan da ake yaɗawa babu gaskiya a cikinsa.

Ƙungiyar ta sake jadadda bukatarta ga sojojin Nijar dasu mayar da Mohamed Bazoum kan mulki nan take.

Kafin wannan sanarwa an jiyo shugaban Ecowas, Bola Ahmed Tinubu yana cewa babu batun a sakarwa sojoji Nijar mara.

Shugaban yace shi baiga wani dalili da zai hana sojojin Nijar koyi da Najeriya ba, ta wannan fuskar.

Gwamnatin sojin Nijar ta buƙaci a bata shekara uku akan mulki, matakin da Ecowas tayi watsi da shi.

Tinubu na waɗannan bayanai ne a lokacin daya ke karɓi bakwacin tawagar malaman da suka je Nijar har sau biyu domin shiga tsakani.

Shugaban na Ecowas yace ba za’a ɗage takunkuman da aka kafawa Nijar ba, har sai sojojin sun miƙa wuya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *