Najeriya da Kanada zasu haɗa kai domin ƙarfafa dimokuraɗiyya a Afirka – Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu ya tattauna ta waya da Firaministan Kanada Justine Trudeau, inda suka duba halin da dimokuraɗiyya ke ciki a Afirka.

A cewar fadar shugaban kasa, Bola Tinubu da Mista Trudeau sun amince cewa zasu mayar da hankali wajen ƙarfafa mulkin dimokuraɗiyya a Afirka.

Shugaba Tinubu ya bayyanawa takwaran nasa ra’ayinsa game da halin da ake ciki a Nijar da Gabon

Yayinda dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa suka hamɓarar da gwamnatin Mohamed Bazoum na Nijar a watan Yuli, irin sune suka hamɓarar da gwamnatin Ali Bongo a Gabon a ranar Laraba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *