Tinubu ya umarci sabbin ministocinsa dasu zage damtse domin kawo sauye-sauye masu kyau ga rayuwar ‘yan kasar nan

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya umarci sabbin ministocinsa dasu zage damtse domin kawo sauye-sauye masu kyau ga rayuwar ‘yan kasar nan.

Ya bayar da umarnin ne yayin taron majalisar zartarwarsa ta farko daya jagoranta a ranar Litinin a fadar shugaban kasar dake Abuja.

Taron ya mayar da hankali kan cimma muradan gwamnatin shugaba Tinubu na samar da hanyoyin cigaban tattalin arziki da wadata al’ummar Nijeriya da kuma kawo karshen talauci tare da jaddada muhimman ayyukan dake gaban gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *